8 Oktoba 2014 - 19:10
Isil: Fada tsakanin Kurdawa da 'yan ta'addar Iraki da Syria ya isa kasar Jamus

Yakin Kurdawa da ‘yan ta’addar kungiyar Isil ta kawancen wahabiya da ‘yan ba’asiyya ya isa kasar Jamus.

Rahotannin da su ke fitowa daga birnin   na kasar Jamus ya ce an yi fada a tsakanin Kurdawa mazauna kasar Jamus da kuma masu akidar Salafiyya a tsawon daren jiya wanda ya yi sanadin jikkatar wasu da dama. Fadan bangarorin biyu ya yi sanadin rufe babbar cibiyar jiragen kasa na kasar Homborg da kuma wasu hanyoyi. Majiyar ‘yan sanda ta ce bangarorin biyu sun yi amfani da wukake da sanduna a fadan, abinda ya yi sanadin jikkatar mutane 12. “Yan sanda sun yi awon gaba da mutane 22 da su ka yi amfani da makamai a yayin fadan. A garin Sleah da shi ma ya ke a kasar ta Jamus an yi  wani fadan a tsakanin Turkawa a gefe daya, da kuma Kurdawa da mabiya addinin Izedeen a daya gefen. ABNA